Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na mallakin Birtaniya, British Airways, ya kaddamar da wani bincike kan wani bidiyo da bayyana, inda daya daga cikin ma'aikatan jiragensu ta yi wasu kalaman da ake danganta su da na nuna wariyar launin fata kan 'yan Najeriya.
Ma'aikaciyar dai ta dauki bidiyon kanta ne a yayin da take kan hanyarta ta zuwa filin jirgi inda a ranar za ta yi aiki da jirgin da zai tafi Abuja babban birnin Najeriya daga filin jirgin sama na Heathrow da ke London.
A wani sako da kamfanin BA ya aikewa BBC ya ce: "Tun bayan da aka jawo hankalinmu kan bayyanar bidiyon, muka fara bincike.
"Ba za mu yarda da kalaman da za su bata wa abokan huldarmu rai ba ko su musguna musu, don haka za mu dauki matakin da ya dace a ko yaushe.
Muna sa ran ma'aikatanmu su zama kwararru a duk lokacin da suke wakiltar British Airways."
Ma'aiakaciyar dai ta dauki bidiyon ne a cikin motarta, inda daga bisani ya yadu a tsakanin abokan aikinta, wadanda su kuma suka sanar da kamfanin halin da ake ciki.
A cikin bidiyon dai matar tana cewa ne, "Yanzu zan hau jirgin wadannan 'yan Najeriyar da za su damu mutum da yi min kaza da kaza, ko kuma a sauya min wajen zama, mazan ma har cewa za su yi suna son a mayar da su wajen da za su sake sosai."
Ma'aikaciyar ta kara da cewa: "Duk 'yan Najeriya za su dinga damunka da ba ni Coca-Cola, ba ni naman shanu shi na fi so. Me ya sa naman ya kare?
"Sai ya kasance ba ni da abin cewa sai, 'Yi hakuri naman ne ya kare.'
Ta kuma ci gaba da cewa: "Wannan dare na Juma'a ba zai min dadi ba don zan yi tafiya da mutanen da ba su da aiki sai damun mutum da tambaye-tambaye ko korafi."
Kafar yada Labarai ta Daily Mail Onlinewacce ita ta fara yada wannan labari, ta ce an bai wa bidiyon suna: 'Ba zan iya da azabar tafiya a wannan jirgin ba."
Tuni dai wannan al'amari ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta na zamani a Najeriya, inda aka dinga mayar da martani ga kamfanin na BA. Ana kuma danganta kalaman matar da cewa kalaman nuna wariya ne.
Da yawan 'yan Najeriya da ke tsokaci kan batun na nuna zallar bacin ransu ne kan abin da matar ta yi, tare da goranta wa kamfanin na BA cewa dama can ba su cika mutunta 'yan Najeriya ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Ma'aikaciyar British Airways Taci Zarafin 'Yan Nigeria A Budiyo
Description : Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na mallakin Birtaniya, British Airways, ya kaddamar da wani bincike kan wani bidiyo da bayyana, inda daya...
Rating :
5