Fira ministar Serbia ta kasance shugabar gwamnati ta farko a wata kasa ta yankin Balkan da ta shiga wani taron gangami na 'yan luwadi da madigo.
Ana Brnabic wadda ita kanta 'yar madigo ce ta yi alkawarin yaki da kyamar da ake nuna wa masu dabi'ar, tare da tabbatar da samar da yanayi na rashin nuna wariya, da kuma mutunta kowa.
Wadanda suka shirya taron sun sabunta kiraye-kirayen da suke yi na yin dokar da za ta halatta aure ko zamantakewa tsakanin masu jinsi daya.
Sannan kuma a dauki matakan kyautata 'yancin masu neman jinsi daya kana da yaki da hare-haren da ake kai wa masu dabi'ar a makarantu.
Shekara bakwai da ta wuce, masu rajin kishin kasa sun farma masu wannan taro, kuma shekara uku bayan nan hukumomi ba su bayar da izinin gudanar da gangamin ba.
Akwai tarin 'yan sanda a wurin macin na ranar Lahadi, ko da yake yawansu bai kai na shekarun baya ba.
Wasu 'yan kalilan din mutanen daban kuma da ke dauke da alamomi da sauran abubuwa na addinin gargajiya na Kirista da tutocin Rasha a gefe daya sun gudanar da zanga-zanga ta hamayya da taron 'yan luwadi da madugon.
Source: BBC Hausa
Title :
Luwadi Da Madigo:Fira Ministar Romania Ta Kafa Tarihi
Description : Fira ministar Serbia ta kasance shugabar gwamnati ta farko a wata kasa ta yankin Balkan da ta shiga wani taron gangami na 'yan luwadi da...
Rating :
5