Dan wasan gaba na Manchester United Romelu Lukaku ya ce yana son magoya bayan kulob din su "mayar da hankali kan wani abu" su daina yi masa eho.
Wata kungiyar da ke yaki da nuna wariyar launin fata mai suna Kick It Out ta bayyana irin ehon, kan girman azzakarin dan wasan mai shekara 24, da cewa "abin kyama ne kuma nuna wariyar launin fata ne".
Shafin Twiter na United ya ambato Lukaku na cewa "Wannan shi ne goyon baya mafi girma da na samu tun da na koma kungiyar".
"Wakar da magoya baya ke yi mai dauke da eho suna yi ne da nufin fatan alheri amma ya kamata su daina. Ya kamata mu rika mutunta juna."
Ita kuwa kungiyar Kick Out, a wani sako da ta wallafa a farkon makon nan, ta ce "Ba za a lamunci yin kalaman nuna wariyar launin fata ba ko da kuwa ana yin hakan ne domin nuna goyon baya ga dan wasa".
United ta wallafa sakonta ne gabanin wasan cin kofin Carabao da suka doke Burton Albion - inda dan wasan dan kasar Belgium, wato Lukaku ya zauna a benchi - cewa " za a dauki mataki kan duk wani mutum da ya yi kalaman nuna kyama", ana tunawa magoya baya cewa kulob din ba zai yarda da nuna wariyar launin fata ba.
An dai ji magoya bayan suna yin eho irin wanda suke yi wa Lukaku a Old Trafford ko da yake sun dan boye wasu kalamai daga ciki.
Kulob din United ya sayi Lukaku daga Everton a kaninitial £75m a lokacin bazara ko da yake za a iya mayar da kudin ya zama £90m.
Ya ci kwalo a biyar a gasar Premier a wasa biyar da ya buga wa kulob din.
Kazalika Lukaku ya ci kwallo a wasan da suka yi da Real Madrid a gasar European Super Cup da suka yi a watan jiya.
Source: BBC Hausa
Title :
Lukaku Ya Bukaci Magoya Baya Su Daina Kyamar Sa
Description : Dan wasan gaba na Manchester United Romelu Lukaku ya ce yana son magoya bayan kulob din su "mayar da hankali kan wani abu" su dain...
Rating :
5