Liverpool za ta daukaka kara kan haramcin daina buga wasa uku da aka yi wa dan wasanta Sadio Mane bayan an kore shi daga fili a wasan da Manchester City ta doke su da ci 5-0.
An kori Mane, mai shekarar 25, daga fili minti 37 da soma wasa bayan ya shuri mai tsaron ragar City Ederson a fuska da kafa.
Dan wasan dan kasar Senegal ba zai buga wasan Premier League da za su yi da Burnley da Leicester ba, da kuma wasan da za su yi a gidan Leicester na cin kofin EFL.
Za a iya rage haramcin da aka yi masa zuwa daya ko biyu idan suka yi nasara a karar da suka daukaka.
Ranar Asabar kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ceda shi da takwaransa na City Pep Guardiola ba su yi zaton za ta kori Mane ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Liverpool Zata Daukaka Kara Kan Mane
Description : Liverpool za ta daukaka kara kan haramcin daina buga wasa uku da aka yi wa dan wasanta Sadio Mane bayan an kore shi daga fili a wasan da Man...
Rating :
5