Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce babu littafin adabin Bahaushe da ya kai tasirin Magana Jari ce.
Farfesan wanda shi ne shugaban jami'ar karatu daga nesa wato National Open University a Najeriya, ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan.
A makon jiya ne aka gudanar da wani taro a garin Saint Andrew a yakin Scotland game da tasirin labaran littafin Dare Dubu da Daya ga al'ummar duniya, kuma farfesan shi ne mutum daya tilo da ya halarci taron daga nahiyar Afirka.
Farfesa Abdallah ya ce littafin Magana Jari Ce ya yi zarra wajen sarrafa labari da kuma nuna akidar Malam Bahaushe.
"Shi ne kadai littafin Hausa da aka fassara zuwa harsunan Larabci da kuma Portuguese," in ji shi.
Ya kara da cewa "ko muna so, ko ba ma so littafin shi ne ya fito da martaba da rayuwar Bahaushe a cikin labari."
Akwai cikakkiyar tattaunawar da Ahmad Abba Abdullahi da farfesan, sai ku latsa alamar lasifika a jikin hoton da ke sama don sauraro.
Source: BBC Hausa
Title :
Littafin Magana Jarice Tafito Da Martabar Bahaushe-Farfesa Abdallah Uba
Description : Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce babu littafin adabin Bahaushe da ya kai tasirin Magana Jari ce. Farfesan wanda shi ne shugaban jami'ar...
Rating :
5