Ruwa ya ci mutum 56 bayan da wani kwale-kwale ya nutse a wani kogi a jihar Nejan Najeriya.
Kwale-kwalen da ke dauke da mutum 60 ya kife ne a Shiroro lokacin da ake ruwa kamar da bakin kwarya.
An ceto mutum hudu daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su, yayin da wani matukin kwale-kwale a yankin ya shaida wa BBC cewar kawo yanzu masu ninkaya sun samo gawarwaki 12.
Ana ci gaba da ayyukan ceto, amman fatan sake samun wadanda suka tsira daga hatasarin na raguwa.
Mutanen da lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar kauye ne a lokacin da hatsarin ya auku a kogin kwara.
Ana yawan samun hatsarin kwale-kwale a Kogin Kwara domin cinkoson mutane kan kwale-kwale mara karfi da kuma bishiyoyin cikin ruwa da suke kwale-kwalen ke cin karo da su.
Source: BBC Hausa
Title :
Kwale Kwale Ya Nitse Da Mutum 56 A Kogi
Description : Ruwa ya ci mutum 56 bayan da wani kwale-kwale ya nutse a wani kogi a jihar Nejan Najeriya. Kwale-kwalen da ke dauke da mutum 60 ya kife ne ...
Rating :
5