Jami'an lafiya a Najeriya, sun ce adadin mutanen da suka kamu da cutar kwalara a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, ya karu fiye da ninki biyu a kwanaki biyar da suka wuce.
Yanzu kimanin mutum dubu daya da dari uku ne suka kamu da cutar.
Mutum talatin da biyar ne kuma cutar ta hallaka kawo yanzu.
Barkewar cutar ya fi kamari ne sansanonin 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.
A babban birnin jihar ta Borno wato Maiduguri, adadin mutanen da suka kamu da cutar ta kwalara ya karu sosai.
Fiye da mutum miliyan biyu da rabi ne rikicin Boko Haram da aka shafe shekara takwas ana yi ya raba da muhallansu.
Source: BBC Hausa
Title :
Kwalara Ta Sauka A Jihar Borno
Description : Jami'an lafiya a Najeriya, sun ce adadin mutanen da suka kamu da cutar kwalara a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, ya karu fi...
Rating :
5