Neymar bai buga wa Paris St-Germain gasar cin kofin Faransa wato Ligue 1 a karawar da ta tashi babu ci da Montpellier a ranar Asabar, sakamakon jinya da yake yi.
Dan wasan ya koma PSG da taka-leda kan fam miliyan 200 daga Barcelona a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya a fagen tamaula.
Sai dai ana rade-radin cewar dan wasan na tawagar Brazil yana karbar fam 88,552 a kowacce rana, kimanin fam miliyan 2,718,126 a duk wata.
Mujallar Der Spiegel ce ta fitar da wannan rahoton inda ta kara da cewar Neymay yana karbar fam 3,542 a duk sa a daya kamar yadda Marca ta wallafa.
Wata mujallar Paris match ta ce an girke jami'an tsaro da suke kula da lafiyar Neymar a katafaren gidansa da ke kilomita 14 tsakaninsa da wurin atisayen PSG.
Source: BBC Hausa
Title :
Kunsan Nawane Albashin Neymar A PSG?
Description : Neymar bai buga wa Paris St-Germain gasar cin kofin Faransa wato Ligue 1 a karawar da ta tashi babu ci da Montpellier a ranar Asabar, sakama...
Rating :
5