Shugaban Amurka Donald Trump ya sabunta gargadinsa ga Koriya ta Arewa bayan ministan wajen Korea ya yi kalamai masu zafi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Asabar.
Ri Yong-ho ya bayyana Mr Trump a matsayin mutum "mai tabin hankali da ke yunkurin halaka" jama'a.
Shugaban na Amurka ya yi raddi ga Mr Ri da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un da cewa idan suka ci gaba da barazanarsu, nan gaba kadan "za a yi ba su".
Wannan sabuwar takaddama ta taso ne bayan jiragen Amurka masu luguden bama-bama sun yi shawagi daf da gabar tekun da ke gabashin Koriya ta Arewa, karon farko cikin karni na 21.
Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce ta dauki matakin ne domin ta nuna irin karfin sojin da take da shi na iya murkushe duk wani mai yi mata barazana.
Hakan na faruwa ne bayan Koriya ta Arewa ta harba makamanta masu linzami sau da dama a 'yan watannin nan.
Duk da wannan tayar da jijiyar wuya, masu sharhi na ganin da wuya kasashen biyu su gwabza yaki kai tsaye.
Source: BBC Hausa
Title :
Korea Da Amurka Zasu Bawa Hammata Iska
Description : Shugaban Amurka Donald Trump ya sabunta gargadinsa ga Koriya ta Arewa bayan ministan wajen Korea ya yi kalamai masu zafi a zauren Majalisar ...
Rating :
5