Tsohuwar ministar kudi ta Nigeria, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce kishin kasa na daga cikin muhimman dalilan da suka sa ta rike mukamin ministar kudi har sau biyu a kasar.
Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana haka ne a wani shirin Turanci na rediyo da BBC ke gabatarwa mai suna "The Conversation" .
Tsohuwar ministar ta ce, mahaifinta ya koyar da ita kishin kasa, dan haka ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta bayar da gudunmuwar da ta dace a lokacin da take rike da mukaman gwamnati.
Dr. Ngozi ta ce, a lokacin da ta rike mukamin minista a farko, ta yi kokari wajen kawo sauye-sauye, wanda har ta kai an samu nasarar yafe wa Najeriya wasu basuka da ake binta.
Tsohuwar ministar ta ce, a lokacin da aka ba ta mukamin minista na farko, ta yi fargaba, saboda rike mukamin ministar kudi ba karamin abu ba ne musamman a kasa kamar Najeriya.
Dr. Ngozi ta ce wa'adinta na farko a kan mukamin minista shi ya fi ba ta wahala, amma ko da ta sake dawowa a karo na biyu, ba ta ji komai ba, saboda ta san abubuwa da dama ke tattare da mukamin ministar kudin da aka sake ba ta.
Source: BBC Hausa
Title :
Kishin Kasana Yasa Na Rike Minista Har Sau Biyu-Okonjo Iweala
Description : Tsohuwar ministar kudi ta Nigeria, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce kishin kasa na daga cikin muhimman dalilan da suka sa ta rike mukamin mini...
Rating :
5