Duk da yake yawancin mutane na ganin kyankyasai abin kyama ne, amma wani matashin dan kasuwa mai suna Rwehura Daniel daga kasar Tanzania ya samo wata hanyar kiwon su da kuma sayar da su ga masu bukata.
Masana sun tabbatar da cewa kyankyasai na da sinadarin gina jiki na protein da yafi na dukkan halittu a fadin duniya.
To ka taba tunanin cewa kyankyasai na da amfani ta bangaren abinci mai gina jiki?
Rhewura Daniel ya sami karfin gwuiwar kiwon kyankyasai masu yawa kuma wannan harkar ta zame masa hanyar kasuwanci mai kawo masa kudaden shiga.
Ga abin da Rwehura Daniel ya ce: "Wannan dabarar ta zo min ne a lokacin da nake neman hanyoyin sarrafa bola domin in samu kudi.
Birnin Dar es Salaam cike yake bola kuma na san zaka yarda da ni cewa inda bola ta yi yawa, akwai kyankyasai ma masu yawa".
Ya kara da cewa, "To a lokacin ne muka yi tunanin cewa kyankyasan na da amfani a matsayin abinci mai gina jiki ga rayuwar dan Adam, kuma wannan damar ta fadada min tunanina, har na kai ga samun karuwar hanyoyin kudaden shiga.
A halin yanzu na zama mai horas da mutane kan dabarun samun kudi daga kasuwancin kyankyasai, kuma ina samun kudaden shiga masu yawa.
Mariam Nyamwaira kwararriya ce dangane da nau'in abinci mai gina jiki a asibitin kasa na Muhimbili, kuma ta ce kyankyasai na iya taimakawa jikin dan Adam fiye da yadda ake tsammani.
"Kyankyaso na da wani sinadarin protein mai gina jiki na musamman wanda ya nunka wanda ake samu a nonon saniya alfanu a kalla sau biyar".
Amma da alama mutanen na da tababa dangane da sanya kyankyasai cikin jerin abinci.
"Sunana Elizabeth. Gaskiya ba zan iya cin kyankyasai ba, kuma ma ina tsoron su ma. Mai zai sa in ci kyankyaso bayan ina iya samun sinadarin protein daga nama ko kifi?"
Shi kuwa James M. cewa yake, "Lallai na taba cin kyankyasai. Na ci su ne a yayin da nake karatu a kasar Thailand. Dandanon su iri daya yake da na fara. Amma na ci ne saboda kwaikwayon al'adar mutanen Thailand, domin su suna cin kyankyasai."
Hukumar Abinci ta Duniya, FAO, ta ce akwai nau'in kyankyasai 4,500 a fadin duniya, amma iri 30 ne ake dauka a matsayin masu datti, kuma hukumar ta ce sauran na da amfani ga rayuwar dan Adam.
Source: BBC Hausa
Title :
Kasan Dasuke Cin Kyankyaso A Afrika
Description : Duk da yake yawancin mutane na ganin kyankyasai abin kyama ne, amma wani matashin dan kasuwa mai suna Rwehura Daniel daga kasar Tanzania ya ...
Rating :
5