Wata mahangar tunanin tsarin zamani da Kate Raworth wato masaniyar tsimi da tanadi ke da tabbacin za ta zama tsohuwar al'ada (da aka daina aiki da ita), ita ce jajircewa wajen bibiyar kowane lamari da ya shafi lafiya, inda za a barta kawai sakaka da nufin kimanta darajarta a kasuwa.
"Tun daga kan illar Kanjamau zuwa kan sauyin yanayin, idan kana so a ji matsalarka, sai ka tuntubi masanin tsimi da tanadi ya yanka maka farashi kan lamarin…"
Ta ce: "Al'ummar da za su zo nan gaba za su yi mamakin yadda muka ta sanya dukiyar da muke hada-hada da ita a cikin gida (kasarmu) a matsayin jigon juya tsarin tattalin arzikin kasa."
Kamar yadda ta fada mini, cewa, "duk da cewa mun san muna kassara dukiyar da muke amfani da ita wajen kyautata zamantakewa da kula da muhalli. Sabanin mu yi bincike don gano hakikanin abin da ke faruwa, sai mu yi murna da hakan, tare da yin bakam cewa babu wata matsala da muka lura da ita."
Masu juya akalar tunani irin su Raworth, na da tabbaci kan faruwar al'amuran da aka yi hasashensu a karshen karni na 21 shi ne daya daga cikin dabarun "kimanta albarkatu" da zai yi matukar tasiri fiye da hada-hadar kudi wajen tantance nasarar al'ummomi.
Ta fahimci cewa a duniya inda "sinadarin Carbon da Nitrogen da mashigin ruwa za su kasance hanyoyinmu na bibiyar tsarin rayuwarmu na kashin kanmu da kasarmu, tare da kula da lafiyarmu da daidaiton tunani da kwanciyar hankali."
Jajircewar Raworth kan lallai sai an sake tunani kan halin da ake ciki a yau wani hangen nesa ne na daban, da marubuci mai rubutun makala a Jaridar Financial Times (Jaridar bin kadin hada-hadar dukiya) ya bijiro da shi lokacin da na tattauna da shi.
Shi kuwa Harford, daya daga cikin masu karancin tunani bisa la'akarin da tsarinmu na kimanta wannan duniyar cewa ya yi a tare kan iyaka ta yadda za a kimanta kaurar mutane a sassan duniya wajen tantance kudin da ake kashewa.
"Mun bai wa kanmu irin wannan 'yancin a duniyar da ta ci gaba kuma muna son nuna damuwa kan wadanda ke fama da talauci," in ji shi.
"Duk da haka muna ganin cewa daidai ne mutumin da aka haifa misali a ce a Somaliya dole ne ya zauna a Somaliya. Kada ya taho Turai ko Amurka, kuma idan wananan mutumin ya fada mawuyacin halin rayuwa, alhakin duk ya rataya a wuya Somaliya, babu abin da ya shafi masu tsaron kan iyakarmu."
"Idan muka duba takaddama kan kudin da ake kashewa da fa'idojin yin kaura, duk da a gaskiya yin kaura na da dan wani alfanu ga mutumin da ya yi kaurar al'amari ne da ba a cika tattaunawa kansa ba."
Shin inda aka haifi mutum zai zame masa makoma (ta samun yalwa da ci gaban rayuwa) nan da karnoni masu zuwa?
Ta yaya za mu yi kokarin kimanta dimbin mutanen da ke kwarara a fadin duniya a matsayin ci gaban mutane, sabanin ayyukan da kasashe ke iya aiwatarwa?
Bisa la'akari da manuniyar bunkasar ci gaba da kare hakkokin dan Adam zuwa kan ingancin rayuwa da kula da lafiya, tuni duniya ta tunkari wadannan al'amuran.
Managarciyar amsa dai ita ce, duk da cewa hanyar da ta fi kyau wajen inganta halin rayuwarmu nan gaba ita ce kara bunkasa, sabanin haka sai mu fuskanci yadda za a saukaka wahalhalun matalauta da wadanda ke tattare da hadarin shiga kunci.
Shi kuwa masanin Falsafa Peter Singer, ya yi nuni da cewa saukaka wahalhalu shi ne mafi a'ala fiye da sauran al'amura da ba su ta'allaka ga mutane kawai ba.
Domin a martaninsa na kai-tsaye cewa ya yin a bijiro da tambayata, "yadda mafi yawancinmu ke wadaka a cikin dukiya, kuma mun ki tabuka komai wajen taimaka wa wadanda ke fama da matsanancin talauci."
Shin wannan ba wauta ba ce karara da ke nuni da cewa nan gaba za a yi tur da dabi'ar, tare da yadda muke yin sakaka wajen kula da dabbobi, al'amarin da nike jij cewa (ina fatan) zai bayyana ga (al'ummar da ke biye mana) a matsayin mugunta tamkar yadda muke ganin juyin wasannin al'adar Romawa a matsayin jahiliya.
Singer ya kafa hujja a aikinsa na sukar lamiri da aiki a aikace.
Shafin sadarwarsa mai taken Rayuwar da za ka iya ceto ya fitar da tsarin saukaka wahalhalu.
Ya jero kungiyoyin aikin jinkai 10 wadanda za ka iya bai wa kudi a yau.
Roman Krznaric, a matsayinsa na mai juya akalar tunani kan al'ada, kuma marubucin littafi kan Tausasawa: Kundin juyin-juya hali.
"Babban rikicin da 'ya'yanmu (da jikokinmu) za su samu kansu a ciki shi ne za su fuskanci matsalar tarwatsewar kyakkyawar zamantakewa," kamar yadda ya fada mini.
"Al'ummomi za su yi ta karkasuwa saboda bunkasar birane da dimbin hada-hadar kasuwanci, al'adar da ke kara hauhawar hawa da saukar matsanancin son rai.
Don magance matsanancin son kai, Krznaric ya bayar da shawarar a fifita tausasawa a jerin kyawawan dabi'un dan Adam: kan bunkasa "kiman maye gurbin sauran mutane tare da fahimtar duniya a ma'aunin tunaninsu."
A matsayin jigon dankon zamantakewar al'umma. Ta hanyar tausasawa ne kawai, a cewarsa za mu samu bunkasa da ci gaba tare da makomarmu tana nan gaba, inda ake ta kara samun karancin albarkatun kasa, tare da karin gogayyar gasa kan wani al'amari da tsare-tsaren ayyukansa suka baje a aikace.
Karshen lamari dai wani abin takaicin da ta yiwu wata rana mu yi nadamarsa shi ne dabi'armu ta wasararai da hadurran da ke tattare da babban bala'i.
Idan ka yi cikakken nazari, tabbas za a fahimci cewa wata rana dan Adam zai fuskanci barazan ko musifa da za ta halaka daukacin al'ummar duniya ko ma ya karar da mu.
Dangane da shirin da muka yi wa wannan rana shi zai fayyace matsayinmu a matsayin wadanda suka tsira.
Wannan ita ce mahangar Nick Bostrom, daraktan da ya kafa Cibiyar nazarin makoma ta gaba ga al'umma a Oxford, kuma mai juya akalar tunani wanda aikinsa ya ta'allaka da auna kimar al'amuran da ka iya kasancewa nan gaba.
"Idan har mutane sun kasance a raye bayan aukuwa mummunan bala'i,"Bostrom ya fada mini cewa, "za su waiwayi baya su yi nazarin mummunan sakaci da muka yi har ya kai mu ga haka, ta yadda za mu rage hadarin da ke tattare da rayuwarmu.
Amma idan al'umma ta kare, kuma babu wanda ya yi saura ballantana a soki lamirin zamaninmu, wannan ba zai sanya mu taba kasancewa abin kyara ko yin tur da mu ba."
Source: BBC Hausa