Kungiyar Kabilar Ibo mazauna Jihohin Adamawa da Kano, sun yi tir tare da la’antar Kungiyar Neman Kafa Biafra ta Nnamdi Kanu, tare da kiran Kanu a matsayin dan muka, mai ja wa uwar sa jifa.
A wata ziyara da su ka kai wa Gwamnan Jihar Adamawa a ranar Juma’a, Shugaban Ibo mazauna Jihar Adamawa, Obinna Ibere, ya shaida wa gwamnan cewa kungiyar IPOB ta haifar wa yankin su koma baya, kuma su babu ruwan su da ita, da kuma duk wani mai goyon bayan su.
Ya ce Nnamdi Kanu dan tayar da zaune tsaye ne, irin wanda tun farko bai ma kamata a ce an bar su sun kai haka ba.
Ibere ya nuna cewa su na goyon bayan gwamnatin Nijeriya kan matakan da ta dauka domin kawo zaman lafiya a kasar nan.
A Kano kuwa, Shugaban Kungiyar Ibo mazauna jihar, Ebenezer Chima ya yi kira ga jama’a da su daina yi wa kabilar Ibo kudin goro har su yi tunanin kowanen su daidai ya ke da Nnamdi Kanu ko ra’ayin su daya.
Ya ce duk wanda ya taka doka to a kalle shi shi kadai a matsayin mai laifi. Chima ya ce su dai mazauna Kano ba su tare da Nnamdi Kanu da ko ma wane ke son a raba Najeriya.
Shi kuwa Shugaban Kungiyar duk wani da ba dan asalin jihar Kano ba, musammam daga kudancin kasar nan, wato Jimpat Ailambe, ya yi kira da a rika duba korafe-korafen jama’a, ta yadda wasu batutuwan ba ma sai an bari har an kai ruwa rana kafin a magance su ba.
Source: Premium Hausa
Title :
Kabilar Igbo Mazauna Kano Da Adamawa Sun La'ananci Nnamdi Kanu
Description : Kungiyar Kabilar Ibo mazauna Jihohin Adamawa da Kano, sun yi tir tare da la’antar Kungiyar Neman Kafa Biafra ta Nnamdi Kanu, tare da kiran K...
Rating :
5