Gwamnonin yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya sun ba da sanarwar haramta ayyukan kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra ta IPOB a daukacin shiyyar.
Shugaban kungiyar gwamnonin, Dave Umahi na jihar Ebonyi, bayan wani taron gaggawa a Enugu ranar Juma'a, ya bukaci kungiyar da sauran kungiyoyi irinta su fayyace abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kuma su aikawa gwamnonin.
"Duk wasu aikace-aikace na kungiyar IPOB yanzu, sun haramta. Ana shawartarta da sauran kungiyoyin da suke jin an yi musu ba daidai ba, su fayyace matsayinsu kan duk wasu batutuwan kasa."
Gwamonin sun hadar da na jihar Abia da na Anambra da na Ebonyi da na Enugu da kuma mataimakin gwamnan jihar Imo.
Sai kuma shugabancin kungiyar Ohaneze Ndigbo mai kare muradan al'ummar Igbo da mataimakin shugaban majalisar dattijai Ike Ekweremadu.
Dave Umahi ya yi kira ga daukacin gwamnonin yankin su tabbatar da aiki da wannan umarni a jihohinsu.
Ya kuma roki Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Allah ya janye dakarun sojin da ke yankin.
Gwamnan ya ce kungiyarsu ta yi imani da hadin kai da dunkuluwar Najeriya waje guda, ko da yake tana bukatar sake fasalin kasar.
A cewarsa: "Muna nanata muradinmu na sake fasalin Najeriya, inda za a rika tattauna dukkan batutuwan kasa don samun masalaha cikin ruwan sanyi da nufin tabbatar da adalci da daidaito ga duk dan kasa."
Ya ce kungiyar tana tuntubar gwamnonin arewacin kasar wadanda suka ba ta tabbacin tsare rayukan mutanensu da ke arewa, har ma sun shirya ziyartar juna don karfafa gwiwa.
"Muna tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa ana gudanar da cikakken bincike a kan duk zarge-zargen kashe-kashe da jikkata mutane gami da sauran abubuwa na rashin bin doka da aka aikata a yankin lokacin hargitsin," in ji Dave Umahi.
Gwamnan ya ce za a dauki matakan da suka dace a kan duk mutumin da aka samu da hannu wajen aikata hakan.
Ya ce gwamnoni a yankin Kudu Maso Gabas sun dauki matakai kwarara don kare rayuka da dukiyar 'yan asali da ma wadanda ba 'yan asalin yankin ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Gwamnonin Igbo Sun Haramta IPOB
Description : Gwamnonin yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya sun ba da sanarwar haramta ayyukan kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra ta IPOB a daukacin shi...
Rating :
5