Wata tawagar gwamnonin arewacin Najeriya, tana ci gaba da rangadin shiyyoyin kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar.
Tawagar tana wannan rangadi ne domin ta kara yayyafa ruwa ga wutar tashin hankalin da aka yi fama da shi a 'yan kwanakin da suka gabata, ta kuma jaddada muhimancin zaman lafiya da tattaunawa kan matsaloli a tsakanin jama'ar sassa daban-daban na Najeriyar.
Tawagar dai tana ziyartar jihohin Ribas da Abiya da kuma Imo ne.
Gwamnan jihar Barno, Alhaji Kashim Shattima ne ke jagorantar tawagar, wadda ta kunshi gwamnonin jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da na Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, da na Filato, Simon Lalong, da kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.
Bayanai sun ce, gwamnonin na arewacin Najeriya a ranar Talata suna jihar Imo, bayan da suka ziyarci jihar Abiya a jiya, inda suka gana da gwamnan jihar da sarakunan gargajiya da shugabannin addini, da kuma 'yan arewa mazauna jihar.
Jama'ar yankin kudu maso gabashin Najeriya da dama dai suna ganin dacewar ziyarar da tawagar gwamnonin arewa suka kai.
Bayanai dai sun ce, wannan ziyara ta tawagar gwamnonin arewacin Najeriya tana da tubarrakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Source: BBC Hausa