Kakakin fadar shugaban kasa, Garba Shehu ya ce gwamnatin tarayya za ta samar wa manoma buhunan taki miliyan 50 kafin karshen wannan shekara.
Garba Shehu ya fadi haka ne a shirin Hannu da Yawa da a keyi duk Asabar a gidan rediyon tarayya na Kaduna.
Ya ce bayan haka gwamnati za ta kara yawan kamfanonin sarrafa taki daga 11 zuwa 18, inda hakan zai sa a samar wa matasa aikin yi a kasar.
Bayan haka kuma ya ce dalilin irin kokarin da gwamnatin tarayya tayi a harkar noma ya sa an sami ci gaba da saukin abinci a kasar yanzu.
” Da buhun masara ya kan kai 20,000 amma yanzu bai wuce 10,000 ba.
Source: Premium Hausa
Title :
Gwamnatin Tarayya Zata Samar Da Buhun Taki Miliyan 50 Ga Manoma
Description : Kakakin fadar shugaban kasa, Garba Shehu ya ce gwamnatin tarayya za ta samar wa manoma buhunan taki miliyan 50 kafin karshen wannan shekara....
Rating :
5