Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya ce munafunci irin na 'yan jam'iyyar APC ne ya sanya mutane irinsu Sanata George Akume suka ce PDP ce ta jefa kasar cikin mawuyacin halin da take ciki.
"Sanata Akume (dan majalisar dattawa na jam'iyyar APC) kamar Mallam Bolaji Abdullahi (tsohon minista a gwamnatin Jonathan), ya manta cewa PDP ta yi mulkin shekara 16 kuma Akume ya zama gwamna karkashin PDP na shekara takwas, kana ya zama sanata a karkashinta shekara hudu.
Shin da mutum ya zama dan APC yake zama waliyyi ko da kuwa ya kwashe shekara 12 a PDP?", in ji Mr Jonathan, a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Tsohon shugaban kasar na yin raddi ne kan kalaman da aka ambato kakakin jam'iyyar APC Mallam Bolaji Abdullahi ya yi cewa babu wanda ya sace kudin Najeriya kamar Mr Jonathan da kuma wanda Mr Akume ya yi cewa PDP ce ta jefa kasar cikin bala'in talauci.
A cewarsa, "Abin takaici ne jam'iyyar All Progressive Congress ta sake yin karya cewa babu wanda ya saci kudin Najeriya kamar tsohon shugaba Goodluck Jonathan.
"Da farko dai ya kamata su sani babu wata kotu da ta kama shi da laifin sata.
"Muna son tunawa APC cewa tsohon shugaban ya taba bayyana cewa ba shi da asusun banki ko kadarori a kasashen waje.
"Kuma akwai kudirin neman bayanai kan kowanne jami'i da Dr. Jonathan ya sanyawa hannu, don haka ina shawartar Bolaji Abdullahi da masu aiko shi su yi amfani da wannan dama wajen binciko hakikanin abin da ya fada".
Mr Jonathan ya bayyana cewa idan ma shi barawo ne kamar yadda suka fada, ya kamata su Bolaji Abdullahi su sani cewa su ma barayi ne domin shi [Bolaji Abdullahi] ya rike mukamin minista a gwamnatin tsohon shugaban kasar tsawon shekara uku cikin sheara biyar da gwamnatin ta yi.
Tsohon shugaban kasar ya ce gwamnatin APC ba ta biyayya ga dokokin Najeriya, yana mai cewa ta ki sakin mutanen da ta tsare duk kuwa da umarnin da kotuna suka ba ta.
"Muna so 'yan Najeriya su lura cewa kotuna sun bayar da umarni ga gwamnati ta saki Kanar Sambo Dasuki da Sheikh Ibrahim el-Zakzaky, a matsayin beli, amma an ci gaba da tsare su. A fili take cewa gwamnatin APC tana zabar irin biyayyar da za ta yi wa kotu", in ji Mr Jonathan.
Source: BBC Hausa
Title :
Gwamnatin APC Munafukace-Jonathan
Description : Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya ce munafunci irin na 'yan jam'iyyar APC ne ya sanya mutane irinsu Sanata George ...
Rating :
5