Wata mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwa ta hallaka mutane takwas tare da raunata wasu akalla 67 a yankin yammacin Romania kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Yawancin mutanen da lamarin ya shafa wadanda ke ciki da kewayen birnin Timisoara ne, inda iskar mai gudun kilomita 100 a sa'a daya ta kayar da bishiyoyi da yaye rufin gidaje da kuma bannata motoci.
A wasu wuraren ta yi sanadiyyar katse wutar lantarki da ruwan famfo na gidajen jama'a.
Magajin garin na Timisoara Nicolae Robu, ya sheda wa wata tashar talabijin ta TV Digi 24 cewa babu wani gargadi da aka yi musu na game da zuwan guguwar, illa dai kawai an sheda musu cewa za a yi ruwan sama.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta Romania ta bukaci mutane da su zauna a gidajensu, sannan su guji zuwa kusa da bishiyoyi da waya da trukun wutar lantarki.
Rahotanni sun ce a yanzu dai guguwar mai tafe da mamakon ruwan sama ta nufi arewa wurin kasar Ukraine.
Source: BBC Hausa
Title :
Guguwa Mai Tsanani Ta Hallaka Mutane A Romania
Description : Wata mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwa ta hallaka mutane takwas tare da raunata wasu akalla 67 a yankin yammacin Romania kamar yadda huku...
Rating :
5