Juma'a rana ce da Hausawa ke yi kirari da Haji, babbar rana. Ba mamaki, idan musulmai suka cika da ɗoki bana, don hawa idin babbar sallah a wannan Juma'a.
Wani fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce ba shakka "ai idi biyu ne suka hadu".
Ya ce idan aka ce yau sallah babba ko sallah karama, kuma yau Juma'a... ranar farin ciki biyu ne suka hadu.
Juma'a, rana ce da musulmai kan taru duk mako a manyan masallatansu don yin sallah raka biyu tare da sauraron huduba.
A irin wannan rana, wasu Musulman ba sa fita aiki, inda suke sadaukar da mafi rinjayen wunin ranar a masallaci.
Ranar tana da dumbin muhimmanci don kuwa Musulmai duk rintsi ba sa yarda su rasa sallar Juma'a uku a jere.
A cewar Sheikh Ibrahim Khalil, babban makasudin idi shi ne sanya wa mutane farin ciki, don kuwa rai dangin goro ne, ban iska yake so. "Dan'adam yana bukatar samun farin ciki lokaci zuwa lokaci.
Ma'anarsa farin ciki wanda yake maimaituwa."
Sheikh Ibrahim Khalil ya ce daga cikin fa'idar sallar idi, akwai ba wa mata da yara damar nishadi, don su more su yi nishadi.
Bikin babbar sallah wadda mutanen da suke da hali ke yin layya, to, ko mutumin da bai yanka dabba ba, zai samu ribar samun kyautar nama ko sadaka, kai hatta kanshin ma, zai sa dan'adam jin dadi, in ji shi.
Sai na yi Juma'a ranar idi?
Malamin ya ce akwai wasu bayanai da aka ruwaito cewa idan yau idin Juma'a, to ba sai musulmi ya je sallar Juma'a a wannan rana, don kuwa ya samu sallar idi. "To ba haka ake nufi ba."
A cewarsa, wannan hukunci ne a kan mutanen karkara da kan yi dawainiyar zuwa maraya don yin sallar idi, kuma a kusa da su, babu masallacin Juma'a.
Don haka aka sawwake musu saboda rage musu yin doguwar tafiya su je maraya don yin sallar Juma'a a ranar idi.
Sheikh Ibrahim Khalil ya ce a yanzu kusan duk kauyuka suna da masallatan Juma'a kuma suna da masallatan idi, don haka yin sallolin guda biyu babbar falala ce da bai kamata musulmi ya bari ta kubuce masa ba.
Ya ambato Annabi Muhammadu (S.A.W) na cewa yau mun yi sallar idi ran Juma'a wanda ya samu damar zuwa sallar Juma'a ya zo wanda bai samu dama ba, ba sai ya zo ba, amma mu za mu yi.
Ya ce tun da Annabi ya ce shi zai yi, to yadda Annabi ya yi shi ne abu mafi cancanta mutum ya yi.
Sai dai ya ce idan mutum ya ce shi ba zai sallaci Juma'a ba ranar idi, ba za a ce bai kyauta ba.
"Don kuwa Abdullahi Bn Zubair ya yi sallar idi ran Juma'a kuma ba a ga ya fito sallar Juma'a ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Farin Ciki Biyu Ya Riski Musulmai
Description : Juma'a rana ce da Hausawa ke yi kirari da Haji, babbar rana. Ba mamaki, idan musulmai suka cika da ɗoki bana, don hawa idin babbar salla...
Rating :
5