Paulo Dybala ya ci kwallo uku rigis a wasa na 100 da ya yi wa Juventus a karawar da ta ci Sassuola 3-1 a gasar Serie wasan mako na hudu a ranar Lahadi.
Dan wasan tawagar kwallon Argentina ya ci ta farko a bugun da ya yi daga wajen da'ira ta 18 da kuma ta biyu a cikin da'irar sannan ya ci ta uku a bugun tazara.
Sassauola ta zare kwallo daya ta hannun Matteo Politano bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.
Dybala ya zama dan wasan Juventus na farko da ya ci kwallo a kowanne wasa hudu da kungiyar ta yi a gasar Premier ta bana.
Haka kuma shi ne na biyu da ya ci kwallo takwas a farkon fara gasar wasa hudu a nahiyar Turai, bayan Wayne Rooney a Manchester United a kakar 2011/12.
Source:BBC Hausa
Title :
Dybala Yaci Kwallo Uku A Wasansa Ta Dari
Description : Paulo Dybala ya ci kwallo uku rigis a wasa na 100 da ya yi wa Juventus a karawar da ta ci Sassuola 3-1 a gasar Serie wasan mako na hudu a ra...
Rating :
5