Korarriyar shahararriyar jarumar fina-finan nan na Kannywood a da yanzu kuma hadda fina-finan kudu Rahma Sadau ta bayyana cewa an so ta fito a wani fim din ta na fina-finan kudu a matsayin yar madigo amma sai ta ki yadda saboda la'akari da daga inda ta fito watau arewa.
Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da jaridar The Guardian a karshen makon jiya inda kuma ta bayyana cewa tayi haka ne kawai bisa la'akari da daga inda ta taso da kuma martaba al'ada da addinin yankin arewa.
Haka nan kuma jarumar ta bayyana rungumar da tayiwa mawaki ClassiQ da tayi sanadiyyar korar tata a matsayin bangaren aikin ta da bai kamata a tsangwameta ba game da hakan.
Daga karshe ne kuma sai jarumar ta kara jawo hankalin mutane da cewa shifa tsoron Allah a zuciya yake don haka ba dai dai bane ba a rika yi mata kallon 'yar iska don kawai tana sana'ar ta.
Source: Naij Hausa
Title :
Dalilin Dayasa Naki Amincewa Nafito A 'Yar Madigo-Rahma Sadau
Description : Korarriyar shahararriyar jarumar fina-finan nan na Kannywood a da yanzu kuma hadda fina-finan kudu Rahma Sadau ta bayyana cewa an so ta fito...
Rating :
5