Chelsea za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan mako na biyar a gasar Premier da za su barje gumi a Stamford Bridge a ranar Lahadi.
Chelsea wacce ke rike da kofin Premier ta yi wasa 26 a gida a ranar Lahadi ba tare da an doke ta ba, inda ta ci 19 ta kuma yi canjaras sau 7.
Ita kuwa Arsenal ta yi rashin nasara a wasa biyu da ta buga a waje a bana, sai dai rabon da ta yi rashin nasara a wasa uku a waje tun fara bude kakar Premier a 1954.
Wannan ne wasa na 59 da kocin Arsenal, Arsene Wenger zai fuskanci Chelsea, karawar da ya fi yi da wata kungiya tun komawarsa Ingila da horar da tamaula.
Wannan ne karo na biyu da kungiyoyin za su kara a bana, bayan da Arsenal ta yi nasarar lashe Community Shield da suka fafata mako daya kafin bude Premier shekarar nan.
Source: BBC Hausa
Title :
Chelsea Da Arsenal Zasu Kece Raini
Description : Chelsea za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan mako na biyar a gasar Premier da za su barje gumi a Stamford Bridge a ranar Lahadi. Chelsea wa...
Rating :
5