Ana sa ran Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai koma kasar ranar Lahadi bayan kammala abin da ya kai shi London.
Shugaban ya tafi London ne ranar Alhamis bayan ya kammala taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a Amurka.
Daya daga cikin jami'an da suka raka shugaban Amurka ya tabbatarwar BBC cewa tsarin tafiye-tafiyen mai gidan nasa ya nuna cewa zai koma kasar ne ranar ta Lahadi.
Kafin tafiyar tasa London, Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata.
Da ma dai fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari zai je London bayan ya kammala taron Majalisar Dinkin Duniya.
Sanarwar da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya aikewa manema labarai ta ce Shugaban "Zai je birnin London a kan hanyarsa ta komawa gida".
Sai dai Mr Adesina bai yi karin bayani kan abin da zai sa Shugaba Buhari zuwa London ba.
Kuma da BBC ta tuntube shi a kan batun, ya ce shugaban kasar zai ya da zango ne kawai a London, yana mai cewa ba zai ce komai ba bayan hakan.
A watan jiya ne shugaban na Najeriya ya koma kasar daga London bayan ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba.
A lokacin da yake jinya, 'yan kasar da dama sun yi masa addu'ar samun sauki.
Amma wasu 'yan Najeriyar sun yi ta zanga-zanga inda suka yi kira a gare shi ya koma Najeriya ko kuma ya sauka daga mulki.
Kwanaki kadan bayan zanga-zangar da suka yi a korar gidan da shugaban ya yi jinya ne, Muhammadu Buhari ya koma kasar.
Masu gangamin sun shaida wa BBC cewa matsin lambar da suka yi ne ya tilasta wa Shugaba Buhari komawa kasar.
A lokacin da ya koma Najeriya Shugaba Buhari, cikin raha, ya yi kira ga masu fafutikar su koma Najeriya kamar yadda ya koma, yana mai cewa yana fatan ba rashin kudi ne ya hana su komawa gida ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Zai Dawo Gida Nigeria Daga London
Description : Ana sa ran Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai koma kasar ranar Lahadi bayan kammala abin da ya kai shi London. Shugaban ya tafi London ...
Rating :
5