Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya zauna da shugaban kungiyar IPOB domin tattaunawa akan abin da kungiyar take nema.
Obasanjo ya fadi haka ne da ya ke hira da mujallar Newsweek.
Ya ce shi bai ga wani laifi ko kaskanci ba zama da Nnamdi Kanu don sanin menene suke bukata.
” Ni ban ga wani laifi ba idan har aka ce za ayi haka. Ni zan so ace hakan ma ya faru.
” Zan so in hadu da Nnamdi Kanu ni kai na in tambayeshi Menene matsalar sa. Ba ma shi kawai ba har da wasu da suke da irin wannan akidar a fadin kasar nan.
” Wadanda suka yi yakin Biafra, ba za su so hakan ya sake faruwa ba. Ni kai na ba zan so in sake ganin irin wannan bala’i ba.
Ya yi kira ga gwamnati da ta mai da hankali wajen sanarwa matasa aikin yi.
Source: Premium Hausa
Title :
Buhari Yazauna Da Nnamdi Kanu A Teburin Sulhu-Obasanjo
Description : Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya zauna da shugaban kungiyar IPOB domin tattaunawa akan ab...
Rating :
5