Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen duniya da su sanya baki a kan takaddamar kasar Koriya ta Arewa da kasashen Yammancin Duniya.
Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 wanda ake yi a birnin New York na kasar Amurka ranar Talata.
Ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta samar da wani kwamiti don warware takaddamar makamin Nukiliyar Koriya ta Arewa.
Ya ce ya kamata kwamitin ya kunshi "wakilai daga ko wane bangare na duniya."
Sauran batutuwan da shugaban ya tabo a jawabinsa sun hada da yaki da cin hanci da dimokradiyya da kuma kyakkyawan shugabanci a nahiyar Afirka.
Bana ne karo na uku da shugaban yake halartar taron wanda ake yi kowace shekara a cikin watan Satumba, inda shugabannin kasashen duniya fiye da 100 ke halarta.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Ya Bukaci A Sulhunta Da Shugaban Korea Ta Arewa
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen duniya da su sanya baki a kan takaddamar kasar Koriya ta Arewa da kasashen Yammancin D...
Rating :
5