Kungiyar Kiristoci ta Najeriya ta yi zargin cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari na yunkurin Musuluntar da kasar.
Sakataren kungiyar Rabaran Musa Asake ne ya shaida wa BBC hakan sakamakon kaddamar da takardun lamuni na Musulunci da gwamnatin Shugaba Buhari ta yi a makon jiya.
Sai dai ministan harkokin wasanni Barista Solomon Dalung ya gaya wa BBC cewa gwamnatin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ce ta fara shirin, yana mai cewa gwamnatin Shugaba Buhari ta kammala shi ne kawai.
"Me ya sa kungiyarmu ta Kiristoci ba ta ce Shugaba Jonathan na yunkurin Musuluntar da Najeriya a wancan lokaci sai yanzu? Ina ganin ba su fahimci shirin ba ko kuma suna so su mayar da shi siyasa", in ji Barista Solomon Dalung.
Amma Rabaran Musa Asake ya ce tun a lokacin gwamnatin Shugaba Jonathan suke yin wannan korafi, yana mai cewa "sau biyu ina gudanar da taron manema labarai a kan wannan batu a lokacin gwamnatin Shugaba Jonathan amma ba a saurare mu ba".
Shi dai tsarin sayar da takardun lamuni na Musulmi, wanda ake kira SUKUK, ya karbu a kasashen da ba na Musulmi ba irinsu Burtaniya, Amurka, China da kuma Rasha.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Nason Musuluntar Da Nigeria-CAN
Description : Kungiyar Kiristoci ta Najeriya ta yi zargin cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari na yunkurin Musuluntar da kasar. Sakataren kungiyar Rabara...
Rating :
5