Malama Hajara yar shekara 22 kuma ita da mijinta suna zaune ne a karamar hukumar Miga da ke jihar Jigawa.
Da ga yi mata albishir din kara aure ai ko sai Malama Hajara ta kwankwadi maganin kashe bera.
Kafin ya gama yi mata illa aka suntumeta zuwa asibitin Jahun, amma inaa, kafin kace kwabo, ta sheka lahira.
Wani makwabcin marigayiyan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai cewa albishir kawai maigidanta yayi mata bai ma kai ga yin auren ba ta hallaka kanta.
Ya ce yaruwanta ta taba yin haka a gidan mijinta inda ita ma ta sha maganin bera amma da yake lokacinta bai yi ba, an ceto ranta da kyar.
Yanzu dai an mika wa iyayen Malama Hajara gawar yarsu su binne.
Source: Premium Hausa
Title :
Wata Mata Takashe Kanta A Jigawa Don Mijinta Yamata Albishir Da Zaimata Kishiya
Description : Malama Hajara yar shekara 22 kuma ita da mijinta suna zaune ne a karamar hukumar Miga da ke jihar Jigawa. Da ga yi mata albishir din kara a...
Rating :
5