Ministan watsa labaran Najeriya ya yi zargin cewa wasu mutane ne da ba sa kaunar Shugaba Muhammadu Buhari ke daukar nauyin 'yan kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra domin su kifar da gwamnatinsa.
A wata sanarwa da ya aikewa manema labarai, Alhaji Lai Mohammed ya ce ''Ya kamata 'yan Najeriya su faminci cewa baa kafa IPOB domin neman 'yancin kowanne mutum ko kungiya ba, sai dai ta zama wani makami da zai wargaza kasar nan da kuma kawar da hankalin jama'a daga ayyukan da gwamnatin Shugaba Buhari ke yi.''
Ministan ya kara da cewa "Wata gamayyar kungiyar mutanen da suka rasa madafa a siyasa da wadanda suka sace kudin gwamnati ne suke daukar nauyin kungiyar IPOB. Sun yi amanna cewa idan suka dauki nauyin wannan kungiya za su iya hargitsa kasar nan da kuma tayar da tarzoma".
Alhaji Mohammed ya nuna mamakinsa kan yadda tayar da hankalin da 'yan kungiyar ta IPOB ke yi ya yi kamari a lokacin da aka zabi gwamnatin Shugaba Buhari, yana mai cewa ''lallai ruwa ba ya tsami banza".
"Ya kamata a tuna cewa a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan, Nnamdi Kanu, ya jagoranci zarga-zargar yaki da Boko Haram da kuma nuna goyon bayan gwamnati a kofar gidan gwamnatin Najeriya da ke London. Yanzu kuma ya rikide ya zama jagoran IPOB da ke son hargitsa kasar nan,'' in ji ministan.
Ministan ya yaba wa rundunar sojin Najeriya saboda ayyana 'yan kungiyar IPOB a matsayin 'yan ta'adda.
A ranar Juma'a ne rundunar sojin ta ayyana kungiyar a matsayin ta ta'addanci.
Wata sanarwa da daraktan watsa labarai na rundunar tsaron kasar Manjo Janar John Enenche ya aikewa manema labarai, ya ce kungiyar, "ta sauya zuwa barazanar tsaro ga kasar".
Ta kara da cewa, "Bayan mun yi nazari a tsanake kan abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan, muna son sanar da jama'a cewa ikirarin da mambobin IPOB ke yi cewa ita ba kungiyar tayar da hankali ba ce ba gaskiya ba ne. Don haka abubuwan da suke yi ta'addanci ne"
Sai dai 'yan kungiyar ta IPOB sun ce su ba 'yan ta'adda ba ne.
Wani dan uwan Kanu mai suna Prince Emmanuel Kanu ya shaida wa BBC ta wayar tarho cewa matakin da sojin suka dauka abin dariya ne.
"Wannan kalami abin dariya ne da ke fitowa daga dakarun soja saboda, na daya, ayyukan da muka kwashe shekara da shekaru sun nuna cewa IPOB kungiya ce mai tafiyar da al'amuranta lami lafiya.
"Mun yi ammana da abin da muke yi kuma muna yin sa yadda ya kamata bisa doka; ba ma kisa ba ma kuma sa wa wani ya yi kisa da yawunmu.
"Niyyarmu ba ita ce takalar yaki ba; niyyarmu ita ce mu fargar da kowa cewa muna cikin ukuba a Najeriya. Kuma irin yadda muke cikin wahala, haka mutane da dama ke cikin mawuyacin hali a arewacin Najeriya. Nnamdi Kanu yana yaki ne da zaluncin da ake yi wa 'yan Najeriya ba ka kawai kabilar Igbo ba".
Source: BBC Hausa
Title :
'Yan Biafara Nason Ganin Bayan Gwamnatin Buhari-Lai Muhammad
Description : Ministan watsa labaran Najeriya ya yi zargin cewa wasu mutane ne da ba sa kaunar Shugaba Muhammadu Buhari ke daukar nauyin 'yan kungiyar...
Rating :
5