Rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa ta ayyana wata kungiyar 'yan aware a matsayin 'yan ta'adda.
A makon da ya gabata ne dai daraktan watsa labarai na rundunar tsaron Najeriya Manjo Janar John Enenche ya aikewa manema labarai wata sanarwa, inda ya ce kungiyar, "ta sauya zuwa barazanar tsaro ga kasar".
Sanarwar ta kara da cewa, "Bayan mun yi nazari a tsanake kan abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan, muna son sanar da jama'a cewa ikirarin da mambobin IPOB ke yi cewa ita ba kungiyar tayar da hankali ba ce ba gaskiya ba ne. Don haka abubuwan da suke yi ta'addanci ne"
Amma kuma yanzu sojojin sun ce sun so ankarar da al'umma ne kawai game da barazanar da kungiyar ke tattare da shi, ba wai sun ayyana su a matsayin 'yan ta'adda ba ne a hukumance.
Dama tun a lokacin da rundunar ta fitar da wannan sanarwa, kungiyar ta IPOB ta ce ita ba kungiya ce ta tashin hankali ba.
Wasu 'yan kasar ma da dama da suka hada da masu fada a ji, sun nuna rashin dacewar sanarwar da rundunar sojin ta fitar tun da farko ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta 'yan ta'adda.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya ce ayyana kungiyar IPOB mai fafatukar kafa kasar Biafra a matsayin kungiyar 'yan ta'adda da sojin Najeriya ta yi, bai dace da kundin tsarin mulkin kasar ba.
Masu sharhi dai na ganin ayyana IPOB a matsayin 'yan ta'adda ka iya haifar da wata matsalar.
Kazalika, sanya su a cikin jerin 'yan ta'adda na nufin dakarun sojin za su fuskanci kungiyoyin 'yan ta'adda uku wadanda suka hada da Boko Haram da tsagerun yankin Naija Delta da kuma su, ko da yake har yanzu rundunar ba ta iya murkushe ko wacce daga cikinsu ba.
A baya-bayan nan dai rikicin kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a yankin Kudu maso Gabshin NAjeriyar ya yi kamari sosai, ta yadda sai da rundunar soji ta tura dakaru yankin don dawo da doka da oda.
Source; BBC Hausa
Title :
Bamucewa IPOB 'Yan Ta'adda Ba-Sojin Nigeria
Description : Rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa ta ayyana wata kungiyar 'yan aware a matsayin 'yan ta'adda. A makon da ya gabata ne dai...
Rating :
5