Tauraruwar matashiyar jaruma Maryam Yahya, mai shekara 20, ta fara haskawa ne a cikin fim dinta na farko wato Mansoor.
A wata hira da Yusuf Ibrahim Yakasai, ta shaida masa ta taka rawar babbar jaruma a fim din duk da cewa shi ne fitowarta ta farko a fina-finan Kannywood, saboda ta kudurci aniyar taka rawar da masu shirya fim din suka umarce ta duk da kasancewarta sabuwar fitowa.
Ta kara cewa ainahi ba ita ce wadda za ta fito a matsayin jarumar fim din ba tun da fari, ta samu zama tauraruwar ne saboda rashin zuwan ainahin jarumar a kan lokaci, kuma daman tana cikin fim din sai dai fitowa biyu kadai aka shirya za ta yi.
Ta ce ''Ali Nuhu ne ya sanya aka zabo mu biyu a cikin wadanda za su yi fitowa ta musamman, ya ba mu rubutaccen labarin fim din muka karanta Allah cikin ikonsa sai na kasance wadda ta yi daidai abin da ya bukata, ka ji yadda akai na zama jarumar fim din Mansoor,'' in ji jaruma Maryam.
Maryam ta kara da cewa: ''Da fari na dan ji tsoro, don ita dayar da aka ba mu labarin muka karanta tare ta ce kawai na je ina ta dari-dari. Ina farawa sai na ga an fara tafi da ihu kawai sai sarki Ali ya ce aje a fara aiki.''
Da aka tambaye ta ko yaya ta ji da aka ce ita ce, za ta zama tauraruwar fim din?
Sai ta kada baki ta ce ''Na ji wani dadi da ba zan iya fasalta yadda na ji ba, amma kam ina cikin tsananin farin ciki a wannan lokacin.'' in ji Maryam.
Source: BBC Hausa
Title :
Ba'a Hada Aure Da Sana'ar Film-Maryam Yahya
Description : Tauraruwar matashiyar jaruma Maryam Yahya, mai shekara 20, ta fara haskawa ne a cikin fim dinta na farko wato Mansoor. A wata hira da Yusuf...
Rating :
5