Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya kalubalanci masu cewa ya yi sata lokacin da yake da rike da mukaman gwamnati su bayar da hujja ko kuma su yi shiru.
Wata sanarwa da ofishin ya fitar ta ambato shi yana cewa, "A ko da yaushe mutanen da ba su da hikima ta yin kasuwanci suna tunanin cewa kowa barawo ne kamar su. Suna ganin cewa wani ba zai iya gina kansa ba ba tare da ya yi sata ba".
Atiku ya kara da cewa zai yi yaki da cin hanci da rashawa "yadda ba a taba yi ba" idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya, yana mai cewa "abin haushi mutanen da suka gaza kawo hujja su ci gaba da yi min zargin cin hanci da rashawa".
"Duk da binciken da aka gudanar a baya domin alakanta ni da cin hanci da rashawa da kuma shari'ar da aka yi wa William Jefferson a Amurka a shekarar 2009, an kammala ba tare da an tuhume ni da cin hanci ba", in ji babban jigon na jam'iyyar APC.
Tsohon dan takarar shugabancin na Najeriya na yin wadannan kalamai ne a daidai lokacin da ya zargi gwamnatin Shugaba Buhari da rashin yin abin a-zo-a-gani wurin magance matsalolin kasar.
Alhaji Atiku Abubakar, wanda bai taba boye kwadayinsa na son shugabancin Najeriya ba, ya ce Shugaba Buhari ya mayar da shi saniyar-ware tun da ya zama shugaban kasa duk kuwa da cewa da kudinsa aka yi amfani wurin yakin neman zabensa.
A kwanakin baya ne dai ministar harkokin mata ta Najeriya, Aisha Jummai Alhassan, ta shaida wa BBC cewa ba za ta sake goyon bayan Shugaba Buhari ba idan ya sake tsayawa takarar shugaban kasa, tana mai cewa "zan goyi bayan uban dakina Alhaji Atiku Abubakar, wanda shi ne ya sa ni a gwamnatin Shugaba Buhari".
Ta sha suka daga wurin magoya bayan Shugaba Buhari bisa kalaman nata, inda takwaranta na ma'aikatar wasanni Mr Solomon Dalung ya yi kira ga shugaban kasar ya sallame ta daga aiki.
Source: BBC Hausa
Title :
Atiku Ya Kalubalanci Masu Cewa Yayi Sata Basuda Hujja
Description : Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya kalubalanci masu cewa ya yi sata lokacin da yake da rike da mukaman gwamnati su bayar ...
Rating :
5