Alexandre Lacazette ya zura kwallo biyu a raga, wanda hakan ya sa Arsenal ta doke West Brom a nasararta ta uku a jere a Premier bana a filin Emirates.
Dan wasan gaban na Faransa, wanda ya ci kwallo a dukkanin wasannin uku na gida, ya fara daga raga ne a minti na 20, bayan da mai tsaron ragar West Brom Ben Foster, ya kade kwallon da Alexis Sanchez ya dauko a wani bugun tazara, ta doki sandar raga ta dawo.
'Yan West Brom sun yi korafi kan fanaretin da suke ganin ya kamata a ba su, tun kafin a zura musu kwallon farko a raga, lokacin da Shkodran Mustafi ya bige Jay Rodriguez.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Arsenal ta samu fanaretin bayan da Allan Nyom, dan kamaru ya doke Aaron Ramsey.
Daga nan ne Lacazette ya buga fanaretin inda ya ci kwallon ta biyu a minti na 67, wadda ita ce ta hudu da ya ci wa Arsenal din tun lokacin da ta siyo shi a kan kudin da ba ta taba kashewa ba wurin sayen dan wasa, fam miliyan 46.5 daga Lyon.
Wannan nasara ta sa Arsenal ta daga zuwa matsayi na bakwai a tebur, maki daya tsakaninta da ta hudu Tottenhma, sannan kuma shida tsakaninta da ta daya Manchester City.
Ita kuwa West Brom, wadda dan wasanta na tsakiya Gareth Barry ya kawar da tarihin dan wasan da ya fi buga wasan Premier, ta koma ta 12, kuma har yanzu kwallo hudu kawai ta jefa a raga a bana.
Barry yanzu ya buga wasan Premier 633, inda ya kawar da tarihin tsohon dan wasan Manchester United Ryan Giggs
Duk da yadda West Brom ta farfado a salon kai harinta, yanzu ta yi wasa biyar kenan ba tare da nasara ba, kuma wasa daya kawai daga cikin 12 na waje na gasar lig ta yi nasara a 2017.
Source: BBC Hausa
Title :
Arsenal Ta Dago Sama Bayan Tasha West Brom 2-0
Description : Alexandre Lacazette ya zura kwallo biyu a raga, wanda hakan ya sa Arsenal ta doke West Brom a nasararta ta uku a jere a Premier bana a filin...
Rating :
5