Hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa, na tuhumar Cologne da Arsenal sakamakon abin da ya faru a lokacin karawarsu a wasan Europa League a daren Alhamis.
Ana tuhumar kulob din na Jamus din da laifi hudu, da suka hada da hayaniyar magoya baya da kuma kunna wuta mai tartsatsi, yayin da ake tuhumar Gunners da rufe hanya.
An samu jinkiri na sama da sa'a daya kafin a fara wasan, sakamakon dubban magoya bayan kulob-kulob din da suka sauka a filin wasa na Emirates ba tare da sun sayi tikitin shiga ba.
Kusan magoya bayan Colegne 20,000 ne suka isa Landan, duk da cewa kulob din Arsenal tikitin mutum 2,900 ya bayar.
Sashen kula da da'a da ladabtarwa na Uefa ne zai dauki mataki kan lamarin a ranar 21 ga watan Satumba.
Source: BBC Hausa
Title :
Arsenal Da Cologne Zasu Fuskanci Hukunci
Description : Hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa, na tuhumar Cologne da Arsenal sakamakon abin da ya faru a lokacin karawarsu a wasan Europa League a dare...
Rating :
5