Rundunar sojin saman Najeriya ta shiga aikin dakile tashin hankali a kudu maso gabashin Najeriya mai suna 'Operation python dance II.'
Wata sanarwar da darakatan hulda da jama'a na sojin saman Najeriya, Olatokunbo Adesanya, ya sanya wa hannu, ta ce kayayyakin aikin da sojin saman Najeriya ta tura wa jami'an aikinta na musamman a Fatakwal sun hada da jirgin yaki kirar Alpha Jet.
Sanarwar ta kara da cewar an tura jirgin yankin ne domin a samar wa sojin kasa kariya ta sama domin inganta aikinsu.
An dai fara aikin dakile matsalolin tsaro a yankin kudu maso gabashin Najeriyar ne ranar 15 ga watan Sataumban 2017.
Sojin saman Najeriyar ta ce yawan wurin da aikin zai shafa da kuma bukatar sojin kasan kasar ne ya sa sojin saman suka shiga aikin.
Source: BBC Hausa
Title :
Antura Jirgin Yaki Yankin Igbo
Description : Rundunar sojin saman Najeriya ta shiga aikin dakile tashin hankali a kudu maso gabashin Najeriya mai suna 'Operation python dance II....
Rating :
5