Sakamakon wata hatsaniya da aka samu a wasu sassan kudu maso gabashin Najeriya kan farmakin da ake zargin masu fafutukar kafa kasar Biafra sun kai wa 'yan arewacin kasar, ranar Talata, gwamnatin jihar Abia ta kafa dokar hana fita da dare tsawon kwana uku a Aba.
Gwamnatin jihar ta kafa dokar hana fitar da dare ne a garin na Aba, daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe, har tsawon kwanaki uku.
A Jihar Rivers ma an samu irin wannan farmaki a kan baki 'yan yankin na arewacin kasar da ke a can a garin Obigbo.
Sai dai rahotanni sun ce an samu lafawar lamarin bayan da hukumomi suka dauki matakan tsaro.
Tun da farko dai rahotanni sun ce lamarin ya samo asali ne a garin na Aba sakamakon wani takun-saka da ake zargin ya shiga tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan kungiyar IPOB, mai fafutukar ballewa daga Najeriya, da kafa kasar Biafra.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Abia, Mista Geofery Ogbonna ya sheda wa wakilin BBC cewa, an tsaurara matakan tsaro a yankin na Aba, don kar a keta doka da tsarin gudanar lamurran yau da kullum.
An kuma tanadi shigen wannan mataki a Umuahiya babban birnin jihar ta Abia, kamar yadda kakakin 'yansa sandan ya ce.
Sai dai yayin da wasu bayanai ke nuna cewa ana zargin mutane akalla hudu ne suka rasa rayukansu wasu da dama kuma suka samu raunuka a harin na Aba, rundunar 'yan sandan ta ki cewa uffan game da hakan.
Can a garin na Obigbo ma na jihar Rivers, wasu rahotanni na nuna cewa mutane akalla takwas aka kashe a farmakin, amma kuma 'yan sanda ba su tabbatar da hakan ba, illa dai sun ce ana bincike.
Ganin yadda ake ta kokarin tashin-tashina tsakanin matasan Ibo masu fafutukar kafa kasar Biafra da jami'an tsaro, da kuma la'akari da irin illar da ke tattare da barkewar hatsaniyar, gwamnonin shiyyar kudu maso gabashin Najeriyar sun kuduri aniyar shiga tsakani.
Har ma sun shirya gudanar da wani taron gaggawa ranar Juma'a kan lamarin.
Source: BBC Hausa
Title :
Ansa Dokan Hana Fitar Dare a Abia
Description : Sakamakon wata hatsaniya da aka samu a wasu sassan kudu maso gabashin Najeriya kan farmakin da ake zargin masu fafutukar kafa kasar Biafra s...
Rating :
5