Hukumar hana fasa kauri ta Najeriya, kwastam, mai kula da shiyyar tashar jiragen ruwa ta Tincan Island da ke a Legas a kudancin kasar, ta kama manyan bindigogi sama da dubu daya.
Shugaban hukumar kustom na kasa kanar Hamid Ali mai ritaya, shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Talata.
Ya kara da cewa an shigo da bindigogin ne daga kasar Turkiya.
Bindigogin sama da 1,000 dai kamar yadda shugaban hukumar kostom ya nuna, ko wacce daya tana iya hallaka mutane da dama a cikin lokaci guda. Koma baya da sauran bindigogi.
Hukumar ta gano cewa bindigogin ana yi musu dure ne da harsashi -- to sai dai ya ce hadarinsu ba ya misaltuwa.
Idan dai ana iya tunawa wannan shi ne karo na uku da rundunar kwastam ta kama bindigogi kusan kira daya. Kuma al'amarin kamen bindigogin ya zama kusan a ko wanne sulusi a wannan shekara.
Bindigogi da aka kama a sulusin farko a wannan shekara dai an shigo da su daga China sai kuma na biyu da na uku aka shigo da su daga kasar Turkiyya.
Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro da suka hada da na kungiyar Boko Haram da masu garkuwa da mutane da kuma masu satar man fetur - da maharan kan yi anfani da bindigogi masu karfi da hanzari.
Hukumar kwastam ta Tincan Island a karkashin Bashar Yusuf, ta gano cewa kwantainar mai makare da makamai da ba ta cikin sahun sundukan kwantainoni da za a tantance, ta yi dabara da taimakon wasu mutane domin budawa kontainar wucewa.
A yanzu haka dai an kama mutum biyu, kuma a nan gaba za a gurfanar da su a gaban kotu.
Shugaban kwastam dai ya nuna kaduwarsa a game wannan wawan kamu, sai dai ya nuna bukatar a fadada bincike da ba kawai zai tsaya ga mutanen da aka kama ba.
A wannan karo zai hada kamfanin da ya taimaka da shigowar makaman.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankama Bindigogi Sama Da dubu Daya A Lagos
Description : Hukumar hana fasa kauri ta Najeriya, kwastam, mai kula da shiyyar tashar jiragen ruwa ta Tincan Island da ke a Legas a kudancin kasar, ta ka...
Rating :
5