Hukumoni a Najeriya sun ce sun kama babban kwamandan kungiyar IS reshen yankin Afirka ta yamman wanda ya kisa kai wa Musulmi hari lokacin bukukuwan babbar sallah.
Hukumar binciken farin kaya ta kasar (DSS) ta ce kungiyar masu tada kayar baya ta IS reshen yammacin Afirka (ISWA) ta shirya ta da zaune tsaye lokacin bukukuwan sallah wanda aka yi a makon jiya.
Kungiyar ta shirya kai hare-hare a jihohin Kano da Kaduna da Neja da Bauchi da Yobe da Borno da kuma babban birnin Tarayya Abuja, kamar yadda wata sanarwar da hukumar ta aike wa BBC ta bayyana.
Sanarwar ta kara da cewa Husseini Mai-Tangaran wanda shi ne babban kwamandan kungiyar shi ne ya kitsa wani mummunan hari da aka kai a jihar Kano a shekarar 2012.
Har ila yau kungiyar karkashin jagorancin Mai-Tangaran ita ce ta kai hare-hare da dama a yankin Arewa-maso-Gasahin kasar wanda yake ci gaba da fama da rikicin Boko Haram, a cewar hukumar DSS.
Kwamanda Mai-Tangaran wanda ake nema ruwa-a-jallo tun a shekarar2012, ya shiga hannu ne a ranar 31 ga watan Agustan bana a Kano.
Hakazalika an kama wani mayakin kungiyar ISWA mai suna Abdulkadir Umar Mohammed a kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, a cewar sanarwar.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankama Babban Kwamandan IS a Kano
Description : Hukumoni a Najeriya sun ce sun kama babban kwamandan kungiyar IS reshen yankin Afirka ta yamman wanda ya kisa kai wa Musulmi hari lokacin bu...
Rating :
5