Hukumomin yankin arewacin India a jihar Uttar Pradesh, sun bukaci a gudanar da bincike, bayan wani dan sanda ya lakadawa wata dalibar jami'ar jihar duka, wadda ke cikin masu boren kin amincewa da cin zarafin mata ta hanyar lalata da su.
Lamarin dai ya fito fili, bayan wasu hotuna da aka yada a shafukan sada zumunta kan yadda dan sanda ya ke dukar dalibar jami'ar Banaras Hindu .
An dai dakatar da dan sanda daga bakin aiki bayan fitowar lamarin. Yayin da dakin kwanan dalibar a jami'ar suka tafi hutun wucin gadi.
Sai dai 'yan sandan sun ce, dole ce ta sanya suka yi amfani da karfin iko ciki har da duka, bayan daliban sun fara tayar da tarzoma.
Sun kara da cewa, daliban sun yi ta jifarsu da duwatsu, da cinnawa motocin mutane wuta, da lalata gine-ginen jami'ar.
Sai dai daliban sun musanta wannan zargi.
Hukumomin jami'ar sun dora alhakin komai kan mutanen da ke wajen jami'ar wanda su ne suka fara rura wutar rikicin.
An ci gaba da zaman dar-dar a yankin Vanarasi inda jami'ar Banaras ta ke, an kuma girke jami'an tsaro a birnin don kwantar da tarzoma.
A ranar alhamis ne dai aka fara zanga-zangar, bayan daliban sun yi zargin hukumomin makarantar sun yi biris da korafin da suka yi na yunkurin cin zarafinsu ciki har da kokarin yin lalata da su.
Daliban sun ci gaba da zanga-zangar lumana har zuwa ranar Asabar, lokacin da 'yan sanda da suke sanya ido kan masu zanga-zangar suka zargi dalibai 100 da suka taru a kofar shiga jami'ar da aikata ba daidai ba.
Sai dai hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta, sun nuna 'yan sanda na dukan daliba da sanda, bayan sun tasa keyar wadandacan daliban.
Kuma da suka zo wajen babu jami'ar tsaro mace ko guda daya da suka zo da ita.
Shugaban jami'ar Girish Chandra Tripathi ya shaidawa BBC Hindi cewa za su gana da matan masu zanga-zangar.
Ya kuma ce hukumomin makaranta za su yi bincike cikin tsanaki dan tabbatar da gano bakin zaren.
Ya kara da cewa watakil a lokacin da daliban suke zanga-zangar 'yan sandan sun ga wani abu da bai da ce ba.
Sai dai daliban sun yi zargin cewa, an karkatar hankali baki daya daga ainahin korafin da suke yi na cin zarafinsu ta hanyar lalata.
Wata daliba mai suna, Akanskha Gupta, ta ce jami'an da ke kula da dakunan kwanan dalibai ba su dauki korafinsu da muhimmanci ba.
''A lokacin da mukai korafin ana kokarin yin lalata da mu, babu abin da aka yi face neman dora mana laifin ta hanyar yi mana wasu tambayoyi marasa kan gado.
Ciki har da wai karfe nawa muke barin dakunan kwanan mu zuwa cikin makaranta da kuma lokacin da muke dawowa.
Saboda Allah wannan ai ba tambaya ba ce, kamata ya yi a bamu damar da za mu amayar da dukkan abubuwan da muke gani ko zarga kafin a san ta inda za a taimaka mana.''
Ita ma wata daliba da bata so a ambaci sunanta ba, ta ce: ''Matsalar cin zarafin mata ba sabon abu bane a nan.
Na yi farin ciki da Allah ya sa dalibai mata sun farga da matsalar tare da daga murya dan aji halin da muke ciki a kawo mana dauki.
Sai dai ana neman a maida abin wata siyasa, kuma hakan bai dace ba.''
A bangare guda kuma, ana shirya gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a manyan biranen India, sai dai kawo yanzu ba a fadi lokaci ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Ana Binciken Yan Sandan Dasuka Lakadawa Dalibai Duka
Description : Hukumomin yankin arewacin India a jihar Uttar Pradesh, sun bukaci a gudanar da bincike, bayan wani dan sanda ya lakadawa wata dalibar jami...
Rating :
5