Hukumomi a kasar Tunisia sun yi watsi da dokar da ta haramtawa mata auren mutanen da ba Muslmi ba.
Wata mai magana da yawun shugaban kasar Beji Caid Essebsi ce ta bayar da sanarwar sannan ta taya matan murna saboda "samun 'yancin da suka yi na auren duk wanda suke so".
Kafin wannan lokaci dai, duk mutumin da ba Musulmi ba da ke son auren 'yar kasar dole ne ya Musulinta sannan ya mika takardar da ta nuna cewa ya Musulinta ga hukumomi.
Ana kallon Tunisia a matsayin daya daga cikin kasashen Musulmi da suka ci gaba wurin bai wa mata 'yanci.
An kaddamar da sabuwar dokar ce bayan Shugaba Essebsi ya bukaci a yi garanbawul ga dokokin yin aure wadanda aka amince da su a shekarar 1973.
A watan jiya ya ce dokokin yin auren kasar sun zama tsohon yayi don haka akwai bukatar yi musu kwaskwarima.
Da ma dai kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasar sun sha yin kira a yi watsi da dokokin, suna masu cewa sun sabawa 'yancin mutum na zabar dukkan wanda yake so ya aura.
Source: BBC Hausa
Title :
An Amince Matan Tunisia Su Auri Mazan Daba Musulmi Ba
Description : Hukumomi a kasar Tunisia sun yi watsi da dokar da ta haramtawa mata auren mutanen da ba Muslmi ba. Wata mai magana da yawun shugaban kasar ...
Rating :
5