Lil Ameer, wanda ake yi wa lakabi da dan autan mawakan hip hop na Hausa ya rasu.
Mawakin, wanda ya yi fice a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ya rasu ne sakamakon hatsarin mota.
Lil Amir ya yi wakoki da dama kuma masana harkokin fina-finan Kannywood irin su Farfesa Abdallah In a Adamu sun sha yin sharhi kan wakokinsa.
Dan autan mawakan yana da kyakkyawar alaka da fitaccen jarumin fina-finan na Kannywood Adam Zango wanda ke yawan yabonsa.
A sakon ta'aziyyar da ya wallafa a shafinsu na Instagram, Adam Zango ya yi addu'ar cewa "Allah ya jikanka karamin dan uwana. Allah ya sa Aljanna makoma. Kai duniya ba a bakin komai take ba!"
Sauran fitattun jarumai da masana harkokin fina-finan Kannywood irinsu Ali Nuhu da Ibrahim Sheme da makamantansu sun yi addu'ar Allah ya gafarta Lil Amir.
Fitattun wakokin da marigayin ya rera sun hada da "Kai Matsa Mana", "Dance for me", da sauransu.
Source: BBC Hausa
Title :
Allah Yayi Rasuwa Wa Dan Autan Mawakan Hip Hop Na Hausa
Description : Lil Ameer, wanda ake yi wa lakabi da dan autan mawakan hip hop na Hausa ya rasu. Mawakin, wanda ya yi fice a jihar Kano da ke arewacin Naje...
Rating :
5