Shugaban hukumar alhazan Najeriya (NAHCON) Abdullahi Muktar ya ce an kammala kwashe maniyyatan kasar wadanda suka yi rijista ta hannun jihohi su kimanin 65,000 ranar Lahadi.
"Ba wani alhajin jiha yanzu da ya rage duk an riga an kai su Saudiyya," kamar yadda ya shaida wa BBC ta waya yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya ranar Litinin.
Ya ce adadin alhazan ya dara wanda aka samu bara, don bara alhazai kimanin dubu 61 suka sauke farali.
Sai dai ya ce yawancin mahajjatan kasar na bana manoma ne.
Har ila yau, ya ce a ranar Litinin ne ake saran kammala jigilar alhajazan kasar su kimanin 16,245 wadanda za su je Saudiyya ta hannun kamfanoni masu zaman kansu.
Kimanin Musulmin duniya mutum miliyan daya da dubu dari bakwai ne za su yi aikin hajjin bana.
Za ku iya sauraron cikakkiyar tattaunawar da abokin aikinmu, Haruna Mararrabar Jos ya yi da shi, idan kuka latsa alamar lasifika da ke hoton sama.
Source: BBC Hausa
Title :
Yawancin Alhazan Nigeria Manoma Ne-Abdullahi Mukhtar
Description : Shugaban hukumar alhazan Najeriya (NAHCON) Abdullahi Muktar ya ce an kammala kwashe maniyyatan kasar wadanda suka yi rijista ta hannun jihoh...
Rating :
5