Ana tsammanin yawan mutanen Afirka zai rubanya nan da shekarar 2050, amma kasar Nijar wadda aka fi yawan haihuwa a duniya, yawan al'ummarta za su ninka har sau uku.
A Nijar, kusan duk mace na haifar 'ya'yan da yawansu ya kai shida zuwa bakwai - ko da yake, yawan haihuwar ya zarce hakan a kauyukan Zinder.
Babu mamaki, lamarin ya fi gaban lissafi, domin kusan kowanne kauye ka je - akwai yara ko'ina.
Hatta yaran ma suna da yara - fiye da rabin 'yan mata suna aure kafin su kai shekara 15 a duniya.
Yayin da tattalin arzikin kasashe ke bunkasa kuma mutane ke daɗa arziki, yawan 'ya'yan da ake haihuwa na raguwa, amma Nijar na cikin jerin kasashen duniya da suka fi talauci.
"A Nijar muna da dabi'a ta kasa wadda ke goyon bayan haihuwa, inda ake ganin haihuwar 'ya'ya a matsayin wata alama ta arziki," in ji Dakta Hassane Atamo, shugaban hukumar tsarin iyali ta kasar.
"Sakamako na farko na irin wannan yawan haihuwa shi ne ba za a iya ciyarwa da kuma ilmantarwa tare da kulawa da dukkan wadannnan 'ya'yan ba a halin yanzu.
"Daga baya kuma, makomar kasar za ta fuskanci barazana, sai dai idan mun yi amfani da albarkar yawan wadannan yara masu tasowa."
Tattalin arzikin kasar ya dogara ne a kan noma - noman, kusan na iya abin da za a ci a gida ne kawai - kuma idan ba an dauki wani kwakkwaran mataki ba, wata dama ce wadda mai yiwuwa ba za a yi amfani da ita ba.
Saboda haka a kauyen Anguwal Gawo, mutane na samun taimako daga waje kan hanyoyin daidaita tsarin iyali.
A cikin filayen gidajen kasa, wasu 'yan mata na zaune suna tattaunawa ba boye-boye kan shirin hana daukar ciki da auren dole ko kuma matsalolin auren wuri tare da haihuwar wuri.
Wuri ne wanda masu aikin agaji ke kira 'wuri mai aminci' ga 'yan mata - kuma wasunsu ba su wuce 'yan shekara 10 da haihuwa ba.
Saratou Kanana, mai shekara 27, daya ce daga cikin 'yan mata uku da aka ba wa horo domin jagorancin tattaunawar.
Tana da 'ya'ya hudu, amma duk da maganar ba da tazara tsakanin haihuwa da haihuwa, ba za ta iya fadar 'ya'ya nawa take son ta kara haifa ba.
"Ya danganta da abin da Allah ya yi," in ji ta. Amman lamarin ya fi hakan sarkakiya.
Bayan ta kauce wa wata tambayar da aka yi mata ta hanyoyi daban-daban, tafintan sai ya yi bayani daga baya..
A matsayinta na mace ba ta da zabi. Komai ya dogara da mijinta. Idan mijinta ya yanke shawarar daina haihuwa, sannan ne za ta iya zuwa cibiyar kula da lafiya domin dakatar da haihuwa.
"Amma komai ya danganta ne da mijin. Miji shi ne mai iko."
Source: BBC Hausa
Title :
Yawan Haihuwa Ne Silar Talauci A Niger
Description : Ana tsammanin yawan mutanen Afirka zai rubanya nan da shekarar 2050, amma kasar Nijar wadda aka fi yawan haihuwa a duniya, yawan al'umma...
Rating :
5