Da alama daya daga cikin manyan abubuwan da 'yan Najeriya za su so ganin Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya yi shi ne ya fatattaki 'miyagun' da suke kusa da shi.
Shugaban mai shekara 74 ya koma kasar ne ranar Asabar bayan kwashe fiye da wata uku yana jinyar cutar da ba a bayyana ba a Landan.
Gabanin komawarsa gida, al'amura daban-daban sun faru wadanda ake ganin da ya na nan to watakila ba za su faru ba.
Gwamnonin jihohin Kano da Zamfara sun shaida wa BBC cewa komawar shugaban kasar za ta sauya al'amura da dama.
Gwamna Abdul Aziz Yari na Zamfara ya ce "Abubuwa da yawa sun ta tasowa wadanda da a ce yana nan ba za su faru ba. Amma mu gwamnoni da mukaddashin shugaban kasa min yi bakin kokarinmu wurin magance su".
Shi kuwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce: "Wasu 'yan siyasa sun zaci ba zai dawo ba shi ya sa aka yi ta samun masu son maye gurbinsa abin da kuma ya sa aka yi ta maganganu tsakanin Kudu da Arewa".
Source: BBC Hausa
Title :
Yaushe Buhari Zai Kori Kurayen Dake Gwamnatinsa?
Description : Da alama daya daga cikin manyan abubuwan da 'yan Najeriya za su so ganin Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya yi shi ne ya fatattaki '...
Rating :
5