Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi ya murna da yadda tattalin arzikin Najeriya ke habaka, wani masanin tattalin arziki a kasar ya ce shi bai ga abin da shugaban ya gani ba da ya sa ya furta kalaman ba.
"Mutane a Najeriya ba sa jin dadin tattalin arzikin kasar. Idan aka samu wani wanda ya gamsu da tattalin arzikin kasar, to dan siyasa ne," in ji farfesa kan tattalin arziki da harkar kudi, Ayodele Momodu, a hirarsa da BBC.
Shugaban Najeriyar ya ce shi ya gamsu da yadda tattalin arzikin kasar ke habaka ne bayan ya gana da ministar kudin kasar, Misis Kemi Adeosun, tare da ministan kasafin kudi da na tsare-tsaren kasa, Udoma Udo Udoma da kuma gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ranar Litinin.
Ita ce ganawar farko da ya yi da wadansu manyan mukarraba gwamnatin da ke kula da tattalin arzikin kasar bayan dawowarsa daga jinyar kwana 104 a Landan kan rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
A ganawar ministocin da gwamnan babban bankin Najeriya sun shaida wa shugaban kasar cewar tattalin azrikin kasar na habaka.
Amman kalaman shugaban kasar bayan ganawar sun bata wa wannan farfesan rai, lamarin da ya sa yake tamabayar cewa ko sun ga abun da 'yan Najeriya da kwararru ke gani.
Ga sautin hirar da BBC ta yi da wani masanin tattalin arziki na tambayar ko 'yan siyasar Najeriya na ganin abun da 'yan kasar ba sa gani ne ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi ya gamsu da tattalin arzikin kasar.
Sai a latsa domin a jin yadda hirar ta kasance.
Source: BBC Hausa
Title :
Yan Siyasa Ne Kawai Ke Jin Dadin Nigeria
Description : Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi ya murna da yadda tattalin arzikin Najeriya ke habaka, wani masanin tattalin arziki a kasar ya ce s...
Rating :
5