A cewar rahotanni,maza biyun suna damfarar daliban da suke tausaya masu ta hanyar basu sadaka da zarar sun gansu.
Mazan sun sa kansu a kofar makarantar, inda suke roƙan kudi daga masu wucewa, da sunan cewa su makafi ne kuma basu iya yin komai.
'Yan sanda sun kama makafi biyu da suke bara a jami'ar kasar Imo
An fallasa su ne bayan wani dan sanda ya mari daya daga cikin sannan ya ce mishi ya bude idanunsa, wanda ya aikata hakan.
A Gaskata labarin zuwa Southern City news, daya daga cikin shugabannin dalibai, Chidi Onyeji, ya ce:
" 'Yan sanda da suke haɗe da kofar shiga jami'ar Imo, Owerri sun gano wasu ayyukan dabaru na wata ƙungiya musamman wanda suke karyan cuta dan jawo hankalin juyayi da kuma dalibai masu kirki dan samun sadaka a karkashin inuwar na makanta. "
Bayan wata karin bayani daga garesu, a garin Owerri,'Yan sanda sun bayyana cewa mazan sun yanke shawarar shiga cikin wannan irin halin ne, saboda rashin aikin yi da kuma rashin abinci.
Title :
Yan sanda sun kama makafi biyu da suke bara a jami'ar kasar Imo
Description : A cewar rahotanni,maza biyun suna damfarar daliban da suke tausaya masu ta hanyar basu sadaka da zarar sun gansu. Mazan sun sa kansu a kofa...
Rating :
5