A ranar Juma'a ne shugabannin babbar jam'iyyar adawa ta PDP da na jam'iyyar APC mai mulki suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a fadar gwamnati da ke Abuja.
Tawagogin sun kai ziyarar ne a lokaci daya da misalin karfe 11 na safe, inda Ahmed Makarfi shugaban jam'iyyar PDP ya jagoranci tawagarsa, John Odigie-Oyegun na jam'iyyar APC kuma ya jagoranci tasa tawagar.
Da yake jawabin yi musu maraba, Shugaba Buhari ya nuna matukar godiyarsa da suka samu lokaci duk da irin ayyukan da ke gabansu, suka je yi masa maraba da dawowa gida.
Wannan ziyara na nuna cewa Najeriya kasa daya ce mai hadin kai. Ba taron jam'iyya ba ne. Ba taron siyasa ba ne. Alama ce ta hadin kan kasa. Wannan na nuna cewa dimokradiyyarmu ta halin girma ce," in ji Shugaba Buhari.
Ya kara da cewa, ""Dimkoradiyyar jam'iyyu da yawa ..... Adawa ba ta nufin tashin hankali ko kiyayya ko gaba. Dimkoradiyya na bukatar bangaren hamayya mai karfi amma mai sanin ya kamata.
Shugaban ya kuma bukaci dukkan bangarorin da su mika sakon godiyarsa ga jama'arsu a fadin Najeriya kan addu'o'in da suka yi masa na samun sauki.
Da yake yin nasa jawabin, shugaban jam'iyyar PDP Ahmed Makarfi cewa ya yi, "A shirye PDP take ta yi adawa mai ma'ana. Za mu yi hakan ne don mu tabbatar gwamnatin na yin abin da aka zabe ta ta yi domin amfanin Najeriya baki daya.
"Ba za mu taba yi wa wani fatan rashin lafiya ba, ballatana ga mutumin da aka dorawa nauyin shugabantar kasarmu Najeriya."
Ya kara da cewa, "Muna tabbatar maka da cewa za mu baka hadin kan da duk wata jam'iyyar adawa za ta iya baka, duk kuwa da cewar burin ko wacvce jam'iyyar adawa shi ne ta karbi mulki a hannunta.
Source: BBC Hausa
Title :
Yan PDP Sunje Duba Shugaba Buhari
Description : A ranar Juma'a ne shugabannin babbar jam'iyyar adawa ta PDP da na jam'iyyar APC mai mulki suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari ...
Rating :
5