Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin mayar da martani mai zafi ga duk wata barazana da kasar Koriya ta Arewa take yi wa kasarsa.
Ya ce martanin zai zama "wanda ba a taba ganin irin shi ba a tarihin duniya".
A halin da ake ciki yanzu, Koriya ta Arewa na yin barazanar kaddamar da harin makami mai linzami a yankin tsibirin Guam da ke Amurka, inda mutum 163,000 ke zaune.
Wannan na zuwa ne bayan samun rahoton cewa, Koriya ta Arewa na kokarin samun nasara wajen rage rikicin makami mai linzamin da zai iya shafar wasu kasashe, wani abin da Amurka da kawayenta na Asiya suka dade suna fargabar faruwarsa.
Source: BBC Hausa
Title :
Yakin Amurka Da Korea Zata Iya Kawo Karshen Duniya
Description : Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin mayar da martani mai zafi ga duk wata barazana da kasar Koriya ta Arewa take yi wa kasarsa. Ya...
Rating :
5