Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya yi nasarar cin dukkan wasan karshe bakwai a gasa da ya jagoranci kungiyar.
Kocin ya fara da lashe Kofin Zakarun Turai, bayan da Real Madrid ta doke Atletico Madrid da ci 5-3 a bugun fenariti a San Siro ta Milan din Italiya bayan da suka tashi wasa 1-1 a kakar 2015/16.
Daga nan ne Zidane ya dauki kofi na biyu bayan da ya yi nasara a kan Sevilla a UEFA Super Cup da ci 3-2, sannan ya doke Kashima Antlers a Kofin Zakarun nahiyoyin duniya da ci 4-2 a dai kakar 2015/16.
Da aka shiga shekarar 2017 Real ta lashe kofin Zakarun Turai na 12 bayan da ta doke Juventus da ci 4-1, ta kuma ci Kofin La Liga na 2016/17 sannan ta doke Manchester United da ci 2-1 a UEFA Super Cup.
Kofi na bakwai da Zidane ya lashe shi ne Spanish Super Cup, bayan da ya yi nasarar cin Barcelona 5-1 gida da waje.
Source: BBC Hausa
Title :
Yadda Zidane Yaci kofi 7 A Madrid
Description : Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya yi nasarar cin dukkan wasan karshe bakwai a gasa da ya jagoranci kungiyar. Kocin ya fara da lashe Kof...
Rating :
5