Shuagaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Ahmed Makarfi, ya bayyana cewa suna shirye-shiryen dawo da tsohon shugabankasa, Olusegun Obasanjo, shugaban majalisan dattijai Bukola Saraki da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakarzuwa jam’iyyar su.
A hirar da yayi da yan jaridan PUNCH, Markarfi yace sun kafa kwamitin yin sulhu na kasa baki daya.
“Mu shirya dawo da mutane da dama. Mun kaddamar da kwamitocin sulhu na kasa da na jihohi. Muna rokon Allah ya ba su nasarar dawo da mutane PDP,”Inji shi.
Akan zaben shugabankasa na shekeara 2019, Makarfi yace:“PDP za ta tsayar da dan takara daga Arewa mai karfi wanda zai fuskanci(shugabankasa Muhammadu Buhari) ko duk wanda APC ta tsayar. Dole Buhari sauka a 2019.
“Ba yadda Buari zai kara cin zabe, saboda mun gama duk wani shiryeshiryen kada APC a 2019. Nayi imani da cewa PDP ce za ta lashe zabe muddin ta tsayar da dan takara mai karfi.”
Source: Hausa online
Title :
Yadda zamu dawo da Obasanjo, Saraki, Atiku zuwa PDP - Makarfi
Description : Shuagaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Ahmed Makarfi, ya bayyana cewa suna shirye-shiryen dawo da ts...
Rating :
5