Fiye da mutum 3,000 ne suka rasa muhallansu a bala'in zaftarewar laka da ya faru a Saliyo a makon da ya gabata, wanda ya hallaka akalla mutum 499, inda har yanzu ba a gano inda mutum 600 suka shiga ba.
Wani mai aikin sa-kai Fessellie Marah, ya ce: "Zai yi wahala a san ainihin yawan mutanen da abin ya shafa, saboda wasu gawawwakin ma sun zagwanye. Har yanzu muna zakulo bangarorin jikin mutane a karkashin baraguzai.
Wani bangare na tsaunin Sugar Loaf ne ya rufta kan wata unguwa da ake kira Regent da misalin karfe 05:45 na asubahin ranar Litinin. Hakan ya sa ruwa da laka da duwatsu suka dinga kwararowa daga saman tsaunin, inda suka yi ta rushe gidaje a wasu yankuna biyu daban Kamayama and Kaningo.
Na kidime ina kallon tsauni na ruftawa'
Daga kasan tsaunin a yankin Regent, wani gida da bai gama rushewa ba, ya tsaya a tsakanin sama da kasa.
Wani magidanci Alfred Johnny, na kara-kaina a tsakanin baraguzai yana shan taba kuma yana ta yin waya. Ya rasa abokai uku, wadanda dukkansu suna cikin gidan a lokacin da tsaunin ya rufto.
Ya ce: "Ina zaune ne a karamin gidan da yake baya, " ya fada yana nuna wani dan karamin gida da ya lalace amma bai rushe ba.
"Babban gidan na Yayana ne. Yana zaune a Australiya. Ni ne nake kula da gidan. Wasu ma'aikata biyu da wani injiniya na zaune a ciki.
"Ina tsaye a baranda lokacin da zaftarewar lakar ta afku. Na ji wata kara mai karfi sosai, kamar ana fasa nakiya. Sai duwatsu suka fara zubowa kasa. Daya ya fado kusa da ni har na fadi. Jikina ya hau bari kamar ana kada min gangi.
"Na yi kokarin guduwa na kuma bude kofar gidan ta gaba amma sai duwatsun suka ci gaba da zubowa. Ba zai yiwu na matsa ko nan da can ba.
"Na kidime kawai ina kallon yadda tsaunin nan ke ruftowa. Manyan duwatsu na fadowa gefen gidaje. Ta ko ina mutane sai ihu suke. Ina kallo har sai da ko wanne gida ya rushe," in ji Mr Johnny says.
Ya tafi ya nuna min wajen da ya tsaya yana kallo yayin da rediyonsa, daya daga cikin abubuwa kadan da suka rage masa a gidansa da ya yi ambaliya, ta fara wata waka. Wakar ita ce "Oh Allah ka ceci Saliyo, oh Allah ka taimaki Saliyo, ke ceci wannan kasar da muke so."
Mr Johnny ya yi kokarin kwashee laka da ruwa daga daki daya na cikin gidansa, kuma a nan yake zaune har yanzu. Katifarsa ta lalace don haka kwalaye ya shimfida a kan gadonsa. Kayayyakinsa da laka ta bata kuma ya jibge su a wani dakin daban, inda nan ma laka ta taru a kasa sosai.
'Ina ganin barnar na san cewa na rasa'ya'yana'
Daga sama kadan hanyar hawa tsaunin akwai wani mutum da wata mata suna zaune kan tarin duwatsu. Dukkansu sun yi shiru, suna kallon nesa.
Matar, Yatta Kamara, ta ce: "Na rasa mutum 14 a gidana. Na bar gida a wannan yammacin don na karbo shinkafa daga gidan wata Innata saboda ba mu da abin da za mu ci, kuma ina bukatar ciyar da 'ya'yana.
Allah ya kiyaye
Source: BBC Hausa
Title :
Yadda Yayana 14 Suka Mutu
Description : Fiye da mutum 3,000 ne suka rasa muhallansu a bala'in zaftarewar laka da ya faru a Saliyo a ma k on da ya gabata, wanda ya hallaka akall...
Rating :
5